Malam Abba Wasiri wani mazauni yankin da aka kai harin yace a ranar Asabar ne al’amarin ya faru a kusa da kauyen Kabalewa.
Sojojin na cikin budaddiyar mota kirar Toyota ne suka taka nakiyar a yayin da suke aikin tsaro tsakanin Bosso zuwa Kabelewa.
Kafar talabijin ta Sahel ta tabbatar mutuwar sojojin Nijar shida tare da wasu biyar da suka samu raunuka.
‘Yan Boko haram dai sun dade suna addabar yankin Diffa da ke cikin dokar ta-baci.288